Shugaban kasar Azarbaijan Ilham Aliyev, ya taya zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian murnar nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar da aka yi cikin gaggawa.
A cikin sakon nasa, Aliyev ya gayyaci Pezeshkian da ya ziyarci kasar Azarbaijan domin tattauna makomar ci gaban hadin gwiwar kasashen biyu.
Sakon Aliyev da aka buga a kamfanin dillancin labarai na Azertag shi ne kamar haka.
Ina taya ka murna da zaben da aka zabe ka a matsayin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Muna ba da muhimmanci sosai ga dangantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Azarbaijan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Ina da yakinin cewa, ta hanyar kokarinmu na hadin gwiwa, za mu tabbatar da kara karfafa dangantakar abokantaka da kuma fadada hadin gwiwar moriyar juna tsakanin Azarbaijan da Iran bisa moriyar al’ummominmu da kasashenmu.