Search
Close this search box.

Al-Nakhala: Za mu ci gaba da gwagwarmaya har nasara

Babban sakataren kungiyar Islamic Jihad Ziad al-Nakhalah ya tabbatar a yau Lahadi cewa gwagwarmayar Palasdinawa za ta ci gaba har sai an samu nasara, yayin

Babban sakataren kungiyar Islamic Jihad Ziad al-Nakhalah ya tabbatar a yau Lahadi cewa gwagwarmayar Palasdinawa za ta ci gaba har sai an samu nasara, yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza a wata na takwas.

Al-Nakhalah ya bayyana a yayin taron sakatarorin kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa a birnin Damascus na kasar Siriya cewa al’ummar Palastinu da tsayin dakansu za su ci gaba da fuskantar abokan gaba tare da dogaro da Allah.

Ya ci gaba da cewa al’ummar Palasdinu suna yaki a Gaza kamar yadda ba su taba yin yaki irinsa  ba, kuma mamayar Isra’ila na fuskantar turjiya da ba ta taba fuskantar irin ta ba.

Babban sakataren kungiyar Islamic Jihad ya jaddada cewa tsayin daka shi ne mafificin zabi, duk kuwa da irin sadaukarwa da  rayuka da al’ummar Palastinu suke bayarwa.

Al-Nakhalah ya kara da cewa: Yakin Gaza wata dama ce ga dukkan Falastinawa ‘yan gwagwarmaya wajen tunkarar yahudawan sahyuniya, yana mai cewa wannan yakin jarabawa ce a gare mu baki daya da kuma mutanenmu da ke fama da mamaya da kauracewa gidajensu, yana mai nuni da cewa. ba tare da yakar makiya ba, za mu ci gaba da zama a karkashin mamaya”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments