Al-Adu Da Ci gaban Musulunci A Tarihi 01

001-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da saduwa a cikin shirimmu na ‘al-adu da ci gaban musulunci’ wanda ni Tahir Amin zan ci

001-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da saduwa a cikin shirimmu na ‘al-adu da ci gaban musulunci’ wanda ni Tahir Amin zan ci gaba da kawo maku a wani wani mako sau guda daga sashen hausa na muryar Jumhuriyar musulunci.  Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da a cikin shirin.

///…Madalla, masu sauraro, tunda shirimmu na yau shi ne shiri na farko, muna ganin yakamata mu bayyana manufar wannan shirin da kuma darussan da muke son dauka daga cikinsa.

Da farko al-adu da kuma ci gaban da addinin musulunci ya zowa dana dam da su, musamman musulmi ya zama ni’ama a garesu wand aba zasu iya kwatantashi da kome ba.

Addinin musulunci ya zo da al-adu da kuma ci gaba wadanda suka haskaka tarihin bil-adama, irin hasken da bai taba ganin irinsa ba. Wannan duk da cewa akwai fadi tashi a cikinsu. Haka ma  akwai matsaloli wadanda al-adu da kuma ci gaban addinin musulunci suka faskanta a cikin tarihinsa, duk da haka bai rasa muhimmancinsa da kuma kimarsa ba.

Don haka a cikin wannan shirin zamu yi kokarin bayyanawa masu saurari irin yadda al-adu da ci gaban musulunci ya haskaka rayuwar mutane, musamman musulmi tun bayan bayyanarsa har zuwa yau.

Sai kuma wani abu mai muhimmanci wanda yakamata a sani a nan shi ne, tun kimani karnuka biyu da suka gabata, kasashen yamma sun yi kokarin nunawa duniya, musamman musulmi  kan cewa al-adu da ci gaban su ne kawai ci gaba kuma duk wani ci gaba wanda ba na su ba, ba ci gaba ba ne, ko kuma ci baya ne. Hakama al-adunsu. Wannan tunani ba gaskiya bane, kuma a cikin wannan shirin zamu tabbatar da hakan.

Wannan matsalar tana da mutukar muhimmanci musamman ga ma’abuta falala da Ilmi a duniya. Kan cewa addinin musulunci kyauta ce daga Alla..mahalicci, ga bayinsa ga kuma mutane gaba daya. Ci gaba da sa’adarsu duniya da Lahira yana cikin wannan addinin. Banda haka sanin wannan yana da muhimmanci ga al-ummu masu zuwa, musamman musulmi don su san irin yadda iyayensu suka yi ayyuka  masu yawa suka kuma yaada al-adu da ci gaban da addinin musulunci ya zo da su.

Turawan da kasashen yamma a cikin  karnukan da suka gabata suna son nunawa mutane kan cewa babu wani al-ada ko addini da ya fi al-adu da kuma addinin da suke kansu, wanda ba gaskiya ba ne.

Idan yara sun san irin gwagwarmaya da wahalar da iyayensu suka sha don yada al-aadun addinin musulunci wannan zai yi tasiri sosai a cikin rayuwarsu. Manufar wadan nan kasashe itace, nunawa musulmi da sauran mutanen duniya kan cewa al-adunsu sun dukkan al-adu kuma babu wata wayewa sai ta kasashen yamma. Da haka kuma zasu ga cewa babu makawa sai bin su.

Daya daga cikin manufofin kasashen yamma na kallafawa kasashen duniya al-adunsu, musamman kasashen gabas ita ce, danganta kansu da duk wani ci gaban da aka samu a tarihi ga al-adunsu. Sannan a dayan bangaren kuma suna hana duk wani shi gaban da wata kasa wacce ba kawwayensu ta samu ba.

Dr Shafi’ii Sarustani wani malamin jami’a a nan Iran ya bayyana cewa, kasashen yamma suna amfani da ci gaban ilmin zamani da suka samu da kuma karfin tattalin arziki da suke da shi, (wadan da su ma saboda mulkin mallakar da suka yi wa kasashen duniya na lpkaci mai tsawo) don yada al-adunsu a duniya. Sun yi kokarin dorawa kasashen gabashin duniya, musamman musulmi al-adunsu a matsayin mafi kyawun al-adu.

Kasashen sun kokarin nunawa duniya kan cewa, al-adu da ci gaban bil’adama sun sami asali ne daga wajensu, sun kashe kudade da dukiyoyin don haka.

Saboda haka ya zama lalura ko kuma wajibi ga musulmi, don yada al-adu da ci gaban addinin musulunci su zage dansa don fahintar da musulmi da kuma sauran mutane dangane da daukakan da Allah yayiwa bil’adama a addinin musulunci da al-adunsa.

Samuel Huntington, wani masanin addinai dan kasar Amurka a cikin littafinsa mai suna ‘ Clash of Civilizations’ ko ‘gasar wayewa’ yana kasashen yamma sun ja mutanen duniya zuwa sabbin al-adunsu, banda haka hatta al-adun wasu al-ummu sun maida su nasu, tare da sauya masu sunaye. Suna barin al-adunsu suna maye gurbinsu da sabbin al-adun kasashen yamma.

Kasashen yamma sun dorawa wasu al-ummar al-adunsu don tabbatar da ikonsu a kan wadannan al-ummu a duniya. Wannan ya soma ne tun bayan yakin duniya na biyu, wato a shekara 1946, a lokacinda kasashen yamma sun yi kokarin zama jagororin duniya gaba dayanta.

Sai dai a duk lokacinda suka kasa yada al-adunsu kan wata al-umma, wacce bata son karban al-adun baki, sai su yi amfani da siyasa da karfin soje a wasu lokutan don cimma manufofinsu kamar yadda muke gani yana faruwa a wasu kasashen duniya. 

Mung a yadda wadan nan kasashe suka yi kokarin yada al-adunsu a wasu kasashen da ba kasashen yamma ba, musamman kasashen musulmi, inda a hankali a hankali suke shiga cikin mutane don yada al-adunsu kafin su kafin su tilasta masu ikonsu na siyasa.

Edward Berman, wani marucin kasar Amurka yana fada a cikin daya daga cikin rubuce-rubucensa yana cewa: Kasashen yamma suna amfani da cibiyoyin yada al-adunsu, kafafen sadarwa, musamman ta yadar gizo, da kafafen yada labarai na radiyo da talabijan da jaridu da sauransu don yada al-adunsu, inda suke kokarin samar da akidu da al-adu don ciyarda halayensu da al-adunsu gaba, kuma sun sami nasara a kasashen duniya da dama.

Don haka dole ne idan zamu gudanar da bincike a cikin al-adu da ci gaban addinin musulunci mu kuma kwatantasu da na kasashen yamma, don masu sauraro su bambantasu.

Daya daga cikin muhimman al-amura a al-adu da ci gaba ko wayewar addinin musulunci shi ne, samuwar al-adu nau’ii daban daban a cikinsa. Tarihi ya tabbatar mana da cewa, al-adu masu inganci da tabbata basa sauyawa a duk halin da suka  sami kansu. Suna tabbata tare da dukkan matsalolin da suka gamu da su. Babban misali a nan shi ne, su al-adu da ci gaba ko wayewar addinin musulunci bas a zauyawa, duk tare da fadi tashi ta ta gamu da su a tsawon tarihi, saboda hare-haren makiya kan daulolin musulunci da kuma kokarin mamayarsu da aka yi ta yi a tsawon tarihi.

Banda wannan, al-adu da ci gaba ko wayewar addinin musulunci, ya tattara al-adun wasu al-ummu masu yawa a cikinsa, don haka yafi sauran al-adun tattara nau’o’in al-adu masu yelwa, kamar al-adun larabawa, farisawa da mutanen kasar Masar.  Idan mun kwatanta su da al-adun kasashen yamma zamu ga cewa, suna kokarin shafe wasu al-adun ne su maye gurbinsu da nasu.

A takaice, an amince da cewa, daya daga cikin abinda ya bawa al-adu da ci gaba ko wayewar addinin musulunci kima shi ne karbansa al-adun wasu al-aummun idan har basu sabawa akidu da halayen da addinin ya haramta ba. A addinin musulunci babu bambanci kabila, harshe ko kasar da wani ya fito, sannan addinin baya danganta kansa da wata kabila ta musamman ko kasa ta musamman ko kuma al-adun wasu mutane.

Addinin musulunci addini ne, wanda ya nuna a aikace, yana iya jagorantar bil’adama zuwa ci gaba da daukka a nan rayuwar duniya da kuma bayan mutuwa.

Ba ruwan addinin musulunci da ta’assubanci ko daukan bangare ba tare nuna kabilanci ko harshe ko wata kasa. A farkon bayyanarsa, addinin musulunci ya sami dan’adam yana dab da fadawa cikin rushewar zamantakewa a duniya, ya zo da tunani da amfani da ilmi don kawo ci gaban dan’adam.

A musulunci ana kula da addini ko lahira tare da duniya a lokaci guda, don haka addinin musulunci bai bar ko wani bangare na rayuwa ba face tana magana a kansa ta kuma bayyana hukunci a kansa na korewa ko kuma tabbatar da ita.

Addinin musulunci ya yi watsi da dukkan tunani da halaye marasa kyau a cikin al-adun al-ummun da suka gabata, sannan ya tabbatar da dukkan halaye da al-adu masu kyau dake cikinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted