Babban hafsan hafsoshin sojojin Iran ya sha alwashin yaki da makiya har zuwa cikakkiyar nasara a kansu.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalton Major General Amir Hatami yana fadar haka a jiya Lahadi a lokacinda yake jawabi a taron raya ranakun fursinonin yaki a kallafaffen yaki na shekaru 8 tsakanin Iran da Iraki. Janar Hatami ya yaba da yentattun yaki na shekarun farko na juyin juya hali.
Ya kuma bayyanasu a matsayin gwaraza na farko a kasar. Wadanda suka tsaga a gaban azzaluman shuwagabannin kasar Iraki na lokacinda, wadanda kuma suke samun taimakon dukkan manya manyan kasashen duniya a lokacin.
Kallafeffen yaki na shekaru 8 bayan nasarar juyin juya halin musulunci, abin alfakhari ne ga duk wadanda suka sami halattarsa. Kuma yakin ya zama babban jarrabawa ga mutanen kasar Iran a lokacin saboda al-amura da suka zo daga baya.
Yace tsayawar matasan kasar Iran a gaban kasa Amurka, kasa mafi karfin makamai da tattalin arziki a duniya, wani babban al-amari ne wanda Jagora shahidai ya kodaitar a kansa, karkashin jagora na yanzu Aya. Mojtaba Khaminaei.