Dakarun kare juyin musulunci na Iran ( irgc) sun kore cewa da akwai wata tattaunawa da take gudana a tsakaninsu da Amurkawa.
Mai Magana da yawun IRGC Hussain Muhibbi ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Tasnim” cewa; babu wata tattaunawa da take gudana a tsakaninsu da Amurka ta hanyar wata kafa ta sirri.
Sanarwar ta IRGC dai tana kore abinda shugaban kasar Amurka Donald Trump ya riya na cewa; Suna tattaunawa da jami’an dakarun kare juyin musulunci na Iran.
Kakakin na IRGC ya bayyana furucin na Donald Trump da cewa karya ce tsagwaronta wacce ya gina akan wahami saboda cin kasar da kasarsa ta yi a gaban Iran a yaki.
Haka nan kuma ya ce, dakarun kare juyin musulunci sune takobban jamhuriyar musulunci ta Iran a filin daga, yayin da wani sashen na al’ummar Iran yake kula da harkokin diplomasiyya.
Wani sashe na bayanin kakakin IRGC din ya kunshi cewa; ma’aikatar harkokin wajen Iran ma ta tabbatar da cewa babu wata tattaunawa da take gudana a tsakaninta da Amurka, kuma dalilin hakan shi ne karya alkawali na Amurka wanda take maimaitawa.
Tun da fari kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya kore labaran karya da Amurkan ta watsa na cewa ana ganawar sirri a tsakanin Amurka da IRGC a yankin Arbil na kasar Iraki.