Erdugan: Isra’ila Ce Ke Haddasa Dukkan Yake-Yake A Yankin

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa Isra’ila ce ke haddasa rikice-rikice da yake-yake a Yammacin Asiya, yana mai cewa Ankara ba za ta

Shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyid Urdugan ya bayyana cewa HKI ce mai ruruta wutan yaki a yankin yammacin Asia, kuma duk yake yaken da ke faruwa a yankin tana da hannu.

Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a lokacin da yake hira ta musamman da tashar talabijan ta al-Jazeera ta kasar Qata.

Shugaban y ace kasashen turai shekaru 53 da suka gabata sun ki karba da kuma amincewa da ita a matsayin mamba a kungiyar tarayyar turai, amma a halin yanzu batun shiga cikin kungiyar tarayyar Turai baya daga cikin al-amura masu muhimmanci ga kasar ba.

 A dayan bangaren kuma shugaban ya ce kasar Turkiya ba zata takali yaki da kowa ba, amma ba zata gudu ba idan wani ya nemeta da yaki.

Dangane da Gaza kuma shugaban yace kungiyar Hamaz tana da kekywar niyya, amma HKI bada da wani shiri na samar da zaman lafiya a yankin, don haka ne take ci gaba da kashe falasdinawa, da kuma mutanen kudancin kasar Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted