Tashar talabijin din “Almayadin” mai watsa shirye-shiryenta daga kasar Lebanon ta ce, hare-haren na sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun shafi garuruwan Sur, Bint-Jubail, Nabadhiyyha, da Marja’iyyun. Kuma sojojin mamayar sun yi amfani ne da jiragen sama na yaki da manyan bindigogi sannan kuma da yin kutse da motocin yaki a cikin garuruwan.
A kudancin Lebanon sojojin na mamaya sun yi amfani da jiragen yaki wajen kai hari a garin ‘al-Mansur” dake gundumar Sur.
A garin Bint-Jubail kuwa sojojin haramtacciyar kasar ta Isra’ila sun kai hare-hare ne da manyan bindigogi da kuma a garuruwan Aytarun da Hadasa.
A garin “Marja’iyyun kuwa ‘yan mamayar sun yi kutse ne da motocin yaki su ka shiga cikin titunan garin Bani Hayyan.
A garin Meys-Jabal ma sojojin mamayar sun kutsa da tankokin yakin “Mirkava” da kuma motocin buldoza da su ka rusa wani gida su.
Da jijjifin safiyar yau Litinin ne dai sojojin mamayar su ka kai hare-hare da manyan bindigogi a garuruwan al-mansuri, da Beit Yahun da Dhalusa da kuma Meys-Jabal, haka nan kuma a yankunan Ali Dhahir da Wadi-alsaluqi.
Haramtacciyar Kasar Isra’ila dai ba ta aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a kasar Lebanon,don haka take ci gaba da kai hare-hare babu kakkautawa. A shekaran jiya Asabar sojojin mamayar sun yi kisan kiyashi a kudancin Lebanon wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 11 da kuma jikkata wani adadi mai yawa na mutane.