Yemen: Sojojin Yemen Sun Kai Wa Jirgin Ruwan Yakin Saudiyya Hari

Kakakin sojan kasar Yemen Janar Yahya Sari ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya yi, yana mai kara da cewa, an kai harin
Kakakin sojan Yemen

Sojojin kasar Yemen sun sanar da kai hari akan wani jirgin Ruwan sojojin Saudiyya da kuma wasu kwale-kwalen soja biyu a tekun “Red Sea” kusa da tashar Ruwan “al-makha.”

Kakakin sojan kasar Yemen Janar Yahya Sari ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya yi,  yana mai kara da cewa, an kai harin ne da makamai masu linzami samfurin “Ballastic” wadanda kuma sun sauka akan jiragen Ruwan da aka harba su.

Haka nan kuma janar Sari ya ce, a sanadiyyar harin, jirgin Ruwan ya kone baki daya, yayin da kwale-kwalen biyu su nutse a cikin ruwa.

Bugu da kari, kakakin sojan Sanaa ya ce; suna bin diddigi da kai da komawar sojojin Saudiyya, don haka za  su ci gaba da kai musu hari.

Har ila yau, janar Sari ya ce; matukar Saudiyyar ta ci gaba da killace Yemen, to su ma za su ci gaba da killace ta, da hana jiragenta kai da komowa.

Shi kuwa kamfanin dillancin labarum Yemen “Saba” ya ce sojojin sun kai hare-haren ne akan sansanonin sojan Saudiyya dake a yankin Makha a gundumar Ma’arib ta hanyar amfani da makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuki.

Gwamnatin Sanaa ta sanar da cewa tana cikin Shirin ko-ta-kwana domin fuskantar Saudiyya da yadda  take jibge sojojinta, har zuwa lokacin da Riyadh za ta kawo karshen killace kasar Yemen da ta yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted