Sojojin Mamaya Sun Kutsa Cikin Kasar Syria Tare Da Yin Awon Gaba Da Wasu Samari

Da safiyar yau Litinin ne dai sojojin mamaya su ka kutsa a cikin garin Abidin a yankin Dar'a ta yamma ta hanyar amfani da motocin
Kutsen Isra'ila

Da safiyar yau Litinin ne dai sojojin mamaya su ka kutsa a cikin garin Abidin a yankin Dar’a ta yamma ta hanyar amfani da motocin yaki 10.

Tashar talabijin din “Akhbar-al-Suriya” ta nakalto cewa; Sojojin Mamayar Isra’ila sun kama samari da dama a garin Abidin da su ka kutsa a cikin motocin soja 10.”

Yankin kudancin Syria dai yana fuskantar kutsen sojojin mamayar Haramtacciyar kasar Isra’ila daga lokaci zuwa lokaci tare da takurawa mutanen kauyukan da suka shiga.

A ranar 26 ga watan Yuli ne dai shugaban gwamnatin kasar ta Syria Ahmad Shar, ya bayyana cewa; Kasarsa tana aiki tare da wasu kasashe domin kulla yarjejeniyar tsaro da Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Bayan kifar da gwamnatin Basshar Asad a kasar Syria, sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun lalata dukkanin makaman kasar na sama da ruwa da tankokin yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted