Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya ayyana kyautar kudade ga duk wani da ya kashe sojan Amurka saboda tilasta masu barin yankin gabas ta tsakiya.
Kamfanin dillancin labaran Mehrnews na kasar Iran ya nakalto Janar Hatami yana fadar haka a wani biki da aka gudanar a nan tehran dangane da ranar yan jarida ta kasa. Yace duk wanda ya kashe sojan Amurka ya mika shi ga jami’an tsaron kasar zai sami tuman biliyon 5 ko kuma dalar Amurka $30,000 a matsayin kyauta.
Hatami ya kara da cewa idan macce ce tana da ninkin abinda za’a bawa na miji sannan za’a ajiye makamin da ya yi amfani da shi wajen kashe sojan ko kama shi za’a saye shi ninkin farashinsa a kasuwa sannan a ajiye shi a wurin ajiyar kayan tarihi na kasa.
Ya ce karfin sojen Iran ya karuwa musamman a fafatwar da suke da sojojin Amurka a yakin mashigar ruwa ta Hurmuz. Daga karshe ya ce Amurka ta yi kuskuren da ba zata sake yi ba harabada. A lokacinda ta fadawa Iran da yaki.
Yace Iran zata ci gaba da kare kanta daga makiya dare da rana, karkashin jagorancin Aya. Sayyid Mojtaba Khaminaei.