Yemen Ta Gargadi Saudia Kan Fadada Yaki A Tsakaninsu

Wani babban jami’in gwamnatin Yemen ya gargadi Saudiyya game da fadada yakin da ake yi zuwa cikin kasar, yana mai cewa Yemen na shirin kara

Wani babban jami’a a gwamnatin kasar yemen ya gargadi kasar Saudia dangane da fadada yakin da ake fafatawa da ita zuwa ciki kasar.

Kamfanin dillancin labaran Mehr News na kasar Iran ya nakalto Abdulaziz bin Habto yana wannan gargadinb a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa, gwamnatin Yemen ba zata amince a ci gaba da yaki a cikin kasar yemen kadai ba, don haka ne take korarin tara sabbin matasa masu karfin don tabbatar da tsaron kasar.

Kafin haka dai gwamnatin kasar ta Yemen ta kai hare hare kan matatan man fetur ta Aramco na gwamnatin kasar Saudia a yankin Jizan, inda suka lalata abubuwa masu yawa.

Kamfanin Aramco tana da matatan man fetur wacce take tashe danyen mai ganga 400,000 a ko wace rana, tana kuma da kamfanin sinadaran manfetur a yankin. Kayakin da Aramco take da su a yankin Jizan sun kai dalar Amurka billiyon $21. Sannan yana da injunan bada wutan lantarki har biyu a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted