Shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran a shirye take ta tallafawa mutanen kasar Indonasia bayan girgizan kassan da ta fadawa kasar
Kamfanin dillancin labaran Mehr news na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a wani sakon ta’aziya da ya aikawa shugaban kasar Indonasia a ranar Asabar, ya yi masa jaje kan asarorin da aka yin a rayuka da dukiyoyi sanadiyyar girgizan kasar , yace JMI a shirye take ta tallafawa kasar da abinda ya sawwaka na kayakin agazi da kuma ceton wadanda suke da sauran shan ruwa.
Ya roki All..ta ya gafartawa wadanda suka rasa rayukansu ya kuma gaggauta waraka ga wadanda suka ji rauni.
Mutane kimani 5000 ne suka kaura daga gidajensu bayan da wani girgizan kasa mai karfin ma’aunin richter 7.7 ta fadawa kasar Indonesi a ranar jumma’an da ta gabata. Iyalai kimani 53 girgizan kasar ta shafa.