Shugaban cibiyar kiyasta ci gaban ilimi da bincike da Nazari ta kasashen musulmi ( ISC) ya bayyana cewa; Jamhuriyar musulunci ta Iran ce ta farko a tsakanin kasashen musulmi wajen gudanar da bincike da nazarce-nazarce.
Dr. Sa’id Bakhtiyari ya ambaci fagagen ilimomin da jamhuriyar musulunci ta Iran su ka yi fice da su a tsakanin kasashen musulmi da su ne; kimiyyar kwantum, ilimin na fahimta, kirkirarriyar fasaha da kuma ilimin halittu da kuma sauran ilimomi na zamani masu zurfi.
Kamfanin dillancin labarun “Irna” na Iran ya nakalto Dr. Bakhtiyari yana jawabi a wurin taron karawa juna sani da aka yi a yau Litinin yana cewa; Iran ce ta shige gaban dukkanin kasashen musulmi a jumlace a fagen bincike na ilimomi masu zurfi, haka nan kuma tana zuwa ta biyu da ta uku a wasu fagagen na ilimi.