Wata majiyar sojojin HKI ta bada sanarwan cewa sojojin kasar 18 suka ji Rauni a hare haren kungiyar Hizbullah a kan tuddan Golan na kasar Siriya da ta mamaye.
Majiyar ta kara da cewa daya daga cikin sojojin yana cikin mummunar hali. Tashar radiyo ta sojojin HKI ta bayyana labarin a shafinta na X a jiya Lahadi. Ta kuma kara da cewa dakarun Hizbullah sun kai hare hare kan runduna ta 91 da ke arewacin kasar Falasdinu da ta mamaye da jirgin yaki wanda ake sarrafa shi daga nesa wato Drones, a kan sansanin kuma haren ya lalata sansanin ya kuma jiukata akalla sojoji 18.
Kafin haka dai kungiyar Hizbullah ta bada sanarwan cewa ta kai hare hare kan runduna ta 91 na sojojin HKI a tuddan na Golan, saboda maida martini ga wasu hare haren da jiragen yakin HKI suka kai kan wani gina mai hawa 2 a garin Haula na kudancin kasarLebanon.