Afrika Ta Kudu Ta Bukaci Kotun Duniya,Ta Umurci Isra’ila Ta Dakatar Da Farmaki Kan Falasdinu

Afrika ta Kudu ta bukaci kotun duniya da ta umarci Isra’ila ta dakatar da hare-haren da take kai wa Gaza. Hakan shi ne kawai a

Afrika ta Kudu ta bukaci kotun duniya da ta umarci Isra’ila ta dakatar da hare-haren da take kai wa Gaza.

Hakan shi ne kawai a cewar Afrika ta Kudu ‘’dama ta karshe ta tabbatar da rayuwar Falasdinawa.

A korafin da ta shigar na baya-bayan nan a gaban babbar kotun MDD, Afrika ta Kudu ta ce Falasdinawa na bukatar kariya daga kisan kiyashi.

Afrika ta Kudu ta bukaci kotun da ke birnin Hague da ta dakatar da Isra’ila daga kai hare-hare a Rafah.

Afirka ta Kudun ta kuma zargi Isra’ila da azabtar da Falasdinawa da yunwa ta hanyar hana shigar da kayan agaji yankin.

A kwanan baya Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya jaddada bukatar kara himma a duniya domin kawo karshen zaluncin da ake yi wa Falasdinawa, musamman mata da kananan yara da ba su ji ba ba su gani ba.

A cikin bayanin nasa, ya bayyana cewa, take hakkokin bil’adama mafi muni da “Isra’ila” take yi a kan Falasdinawa ya kai matsayin da ba a taba ganin irinsa ba na zalunci, kiyayya, da wuce gona da iri.

A wani labarin kuma Yau Juma’a ne aka tsara Isra’ila za ta gabatar da bayani a gaban kotun kan aikata kisan kare dangi a Gaza.

Isra’ila dai na mai musanta cewa hare-harenta sun saba wa dokokin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments