Shugabannin Afrika sun yi kira ta bai-daya ta sauya karfin nahiyar a bangaren tattalin arziki da yawan al’umma, zuwa dimbin ayyuka masu samar da riba cikin sauri, da nufin ingiza burikan raya nahiyar yayin da ake fama da rashin tabbas a duniya.
Kiran na gaggawa ya biyo bayan taron nahiyar na 9 kan harkokin kasuwanci na 2026, wanda aka yi a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
Taken taron shi ne, “Zuba Kudi ga Makomar Afrika: Ayyukan Yi da Kirkire-Kirkire da Fasahohi.”
Taron da hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD (UNECA) ke kira duk shekara da hadin gwiwar kungiyar Tarayyar Afrika (AU) da sauran abokan hulda, wani muhimmin dandali ne na tattaunawa tsakanin shugabannin kasashen Afrika da shugabannin bangarori masu zaman kansu da masu zuba jari.
Da yake jawabi ga taron, shugaban Habasha Taye Atske Selassie, ya nanata matukar muhimmancin amfana da karfin matasan nahiyar.