Afirka ta Kudu ta yi kakkausar suka kan yadda Isra’ila ke muzgunawa Falasdinawa tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa don kawo karshen radadin da al’ummar kasar ke ciki musamman mata da kananan yara.
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar ya bukaci kasashen duniya da suka hada da kawayen Isra’ila da kada su rufe ido kan kisan gillar da ake yi wa Falasdinawa a zirin Gaza wanda kawo yanzu ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 35,000 tun bayan fara yakin a ranar 7 ga watan Oktoba.
Ramaphosa ya ce, “Babban take hakkin dan Adam da Isra’ila ke yi ya kai matakin da ba za a iya fahimtarsa ba.
“Dole ne duniya ta kara yin kokarin kawo karshen zaluncin da ake yiwa Falasdinawa, da ba su ji ba ba su gani ba.”
Ramaphosa ya kuma kara da cewa, a ranar Juma’a kasar Afrika ta Kudu ta sake daukar matakin shari’a a kotun duniya ta ICJ, domin neman a ba da umarnin gaggawa na kare al’ummar Palasdinu a Gaza daga keta hakkinsu da ba za a iya misaltawa ba.
Afirka ta Kudu ta kai karar Isra’ila a gaban babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya a watan Disambar bara.
Da farko dai kotun ta ICJ ta zartas da hukunci a watan Janairu, inda ta fitar da wani hukunci na wucin gadi inda ta ce za’a iya danganta abinda Isra’ila ke aikatawa da kisan kiyashi a Gaza.