Search
Close this search box.

Afirka ta Kudu ta bukaci ICJ da ta ba da umarnin gaggawa na dakatar da kisan Falastinawa

Afirka ta Kudu ta yi kira ga kasashen duniya da suka hada da kawayen Isra’ila da kada su yi watsi da kisan kiyashin da ake

Afirka ta Kudu ta yi kira ga kasashen duniya da suka hada da kawayen Isra’ila da kada su yi watsi da kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa a zirin Gaza.

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya jaddada bukatar kara himma a duniya domin kawo karshen zaluncin da ake yi wa Falasdinawa, musamman mata da kananan yara da ba su ji ba ba su gani ba.

A cikin bayanin nasa, ya bayyana cewa, take hakkokin bil’adama mafi muni da “Isra’ila” take yi a kan Falasdinawa ya kai matsayin da ba a taba ganin irinsa ba na zalunci, kiyayya, da wuce gona da iri.

Ramaphosa ya kuma sanar da cewa, kasar Afirka ta Kudu ta mika bukatar gaggawa ga kotun kasa da kasa ta ICJ da ta aiwatar da karin matakan kare al’ummar Palasdinu a Gaza, daga wadannan munanan take hakki.

Ya bayyana cewa, wannan bukata ta Afirka ta Kudu ta zo ne a karkashin yarjejeniyar kisan kare dangi, musamman a matsayin martani ga mamayar da Isra’ila ta yi a Rafah, a kudancin zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments