Search
Close this search box.

 A Kalla Mutane 13 Ne Aka Kashe Sanadiyyar Zanga-zangar Tabarbarewar Tattalin Arziki Da Ake Yi A Nigeria

Rahotannin da suke fitowa daga kasar ta Nigeria sun ambaci cewa; a wasu jahohin da ake gudanar da Zanga-zangar nuna kin amincewa da tabarbarewar tattalin

Rahotannin da suke fitowa daga kasar ta Nigeria sun ambaci cewa; a wasu jahohin da ake gudanar da Zanga-zangar nuna kin amincewa da tabarbarewar tattalin arziki,an sami tashe-tashen hankula wanda ya yi sanadin bude wuta da kashe mutane 13.

Mahukunta sun sanar da cewa; Mutane 4 ne aka kashe a yayin wannan gagarumar Zanga-zangar da ake yi a fadin kasar, an kuma kafa dokar ta baci- a cikin wasu jahohin kasar.

Daraktan kungiyar “Amnesty International” ta kare hakkin bil’adama a Nigeria, Isa Sanusi ya bayyana cewa; Sun sami rahotanni daga shadun ganin ido, da da mutuwar wasu mutanen a cikin wasu jahohi.

Jami’an tsaro sun sanar da kame mutanen da sun kai 300, kamar kuma yadda aka kafa dokokin ta-baci a jahohin kano da katsina, bayan da aka sami sace-sacen duniyar gwamnati.

Jami’an ‘yan sanda sun kuma sanar da cewa an kashe musu daya daya cikin ma’aiaktansu.

Tabarbarewar tattalin arziki, tsadar kayan abinci da karancin kudin shiga da rashin aikin yi, su ne muhimman abubuwan da su ka ingiza mutane fitowa kan tituna domin yin Zanga-zanga.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments