Jiragen Dakon Mai Guda 2 Sun Sabawa Dokokin PGSA

Wasu manya manyan jiragen dakon man fetur guda biyu sun sabawa dokokin wucewa a mashigar ruwa ta Hurmuz amma sun tsira daga haramtasu daga shigowa yankin kwata kwata. Kamfanin dillancin labaran MehrNews na kasar Iran ya bada labarin cewa hukuma mai kula da zirga zirgan jiragen ruwa a mashigar ruwa ta Hurmuz ta bada sanarwan […]

An Wargaza Tawagogin Yan’ta’adda A Tehran, Albos Da Krmansha

Ma’aikatar leken asiri na kasar Iran ta bada sanarwan wargaza wasu tawagogin yan ta’adda dauke da makamai guda biyar da kuma wasu guda uku masu fasa korin makamai zuwa cikin kasar a lardunan Albus da Tehran da kuma Kermanshah. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar tana fadar haka a yau Laraba, […]

Iran ta Sanya Sojojin Agentina Cikin Kungiyoyin Yan Ta’adda

Gwamnatin JMI ta sanya sojojin Ruwa na kasar Agentina da sojojin sama na kasar cikin Jerin kungiyoyin yan Ta’adda a duniya, saboda maida martani ga gwamnatin Argentina wacce ta sanya dakarun IRGC na kasar Iran a matsayin kungiyar yan ta’adda. Tashar talabiojan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar  harkokin wajen kasar Iran na […]

Iran: Tataccen Uranium Ko Kadan Ba Zai Fita Daga Kasar Ba

Sakataren majalisar tsaron kasar Iran Mohsen Rizaei ya  ce Iran ba zata amince makamashin Uranium wanda aka tashe a cikin gida ya bar kasan ba, kuma ko menene karancinsa. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Rezaei yana fadar haka a lokacinda yake hira da tashar talabijan ta Almayadden ta kasar Lebanon a […]

Iran: Zamu Yi Maganar Gurbata Yanayin Da Amurka Da HKI Suka Yi

Shugaban kasar Iran Dr Masuod Pezeshkiya ya bayyana cewa, zai tada batun gurbata yanin da Amurka da HKI suka yi a yake yaken da suka dorawa JMI a taron gurbata yanayin da aka fara a kasar Turkiya a yau Laraba. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau […]

Iran Ta Yi Tir Da Murkushe Masu Zanga-zangar Lumana A Faransa

Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Iran ta yi Allah Wadai da gwamnatin Faransa da ‘yan sanda kasar kan tsauraran Matakai na murkushe masu zanga-zangar da aka gudanar a fadin Faransa kan tsardar rayuwa da hauhawar farashin makamashi da tabarbarewar ayyukan gwamnati. A wata sanarwa da ta fitar hukumar ta bayyana cewa gwamnatin Faransa da […]

Araqchi Ya Ce: Amurka Abar Allah Wadai Ce Saboda Bakar Siyasarta

Ministan Harkokin Wajen Iran ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta yi Allah wadai da tayin Amurka na bayar da lada ga duk wanda ya bayar da bayanai kan shirin Makamashin nukiliya na Iran A cikin wata wasika da ya aike wa Antonia Guterres, Kwamitin Tsaro da Grossi, Araqchi ya yi kira da […]

Ali Ozma’i Ya Jinjinawa Rundunar Sojin Saman IRGC Sabon Gwazonsu

Kwamandan Rundunar Sojojin Ruwa ta Juyin Juya Hali ya bayyana cewa: Mayakan Rundunar Sojan Sama sun tsaya tsayin daka kuma sun iya aiki a lokutan da suka fi wahala A cikin wani sako da ya gabatar a bikin makon rundunar sojin sama, Rear Admiral Ali Ozma’i, Kwamandan Rundunar Sojojin Ruwa ta Juyin Juya Halin Musulunci […]

Reza’i Ya Mayar Da Martani Ga Amurka Kan Jinkirin Bada Amsa

Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran ta mayar da martani da Amurka ta bayar yana cewa yana da ban mamaki Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Janar Mohsen Reza’i, ya nuna cewa: Martanin Amurka na yaudara ne, yana mai cewa: “Sun nemi Amurkawa su bayar da amsa mai haske kuma a bayyane ga sharuddan Iran, […]

Baqa’i: Kisan Gillar Minab Babbar Alama Ce Ta Zaluncin Amurka

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Kisan gillar daliban makarantar Minab alama ce ta zaluncin masu kai hari da kuma nuna juriyar al’ummar Iran Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada bukatar bin diddigin dukkan fannoni na shari’a, ‘yancin ɗan adam da na ƙasashen duniya na harin da Amurka ta kai […]

Qalibaf: Sabon Birnin Makamai Masu Linzami Sako Ne Ga Makiya

Kakakin Majalisar Dokokin Iran ya bayyana cewa: Sabon birnin makamai masu linzami sako ne bayyananne daga Iran ga makiyanta Kakakin Majalisar Dokokin Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya tabbatar da cewa: Sabon birnin makamai masu linzami da Iran ta gina sako ne bayyananne daga Iran ga maƙiyanta. A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Qalibaf ya bayyana […]