Shugaban kasar Iran Dr Masuod Pezeshkiya ya bayyana cewa, zai tada batun gurbata yanin da Amurka da HKI suka yi a yake yaken da suka dorawa JMI a taron gurbata yanayin da aka fara a kasar Turkiya a yau Laraba.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Laraba a lokacinda yake bankwana da Jami’an gwamnatinsa kafin ya shiga jirgi don halattan taron an Antoliyo.
Shugaban ya bayyana cewa, Amurka da kuma HKI duk sun ga sakamakon yake yaken da suka dorawa JMI a zabukan da aka gabatar a kasashensu. Sannan zai tada batun gurbatan yanin da wadannan kasashen biyu suka jawo a kasar Iran da kuma yankin yammacin Asia saboda yake yaken.
Zai tada batun a taron gurbatan yanin na MDD karo na 31 wato ’31st United Nations Climate Change Conference (COP31.
A shafinsa na X kuma shugaban ya, gwamnatin Amurka tana riya cewa tana yakar Iran ne don hanata mallakar makaman Nukliya, inda ta yi amfani da makami mai suna prSM a kan wani wuri a Lameh na kasar Iran haka ma tana maganar amfani da ‘uwar boma boma a kan kasar nan gaba. Don tilastawa Iran abinda ya kira sulhu na dole. Pezeshkiyan yace Kasashen Turai ma suna da hannu a yake yaken da aka dorawa JMI. Suna magana kare hakkin bil’adama da sulhu al-hali abinda suke aikatawa daban ko kuma sabanin maganarsu.
A wannan taron dai ana saran wakilan kasashe 196 ne zasu halarci taron, 71 daga cikinsu shuwagabannin kasashe da shuwagabannin gwamnatoci. Sannan zai gana da wasu wakilai ko shuwagabannin kasashen da zasu halarci taron daga ciki har da Rajab Tayyib Ordugan mai masaukin baki.