Iran ta Sanya Sojojin Agentina Cikin Kungiyoyin Yan Ta’adda

Gwamnatin JMI ta sanya sojojin Ruwa na kasar Agentina da sojojin sama na kasar cikin Jerin kungiyoyin yan Ta’adda a duniya, saboda maida martani ga

Gwamnatin JMI ta sanya sojojin Ruwa na kasar Agentina da sojojin sama na kasar cikin Jerin kungiyoyin yan Ta’adda a duniya, saboda maida martani ga gwamnatin Argentina wacce ta sanya dakarun IRGC na kasar Iran a matsayin kungiyar yan ta’adda.

Tashar talabiojan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar  harkokin wajen kasar Iran na fadar haka a safiyar yau Laraba ta kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Agentina ta bayyana adawarta ga JMI , a lokacinda ta sanya dakarun IRGC a matsayin yan ta’adda, bayan ta san cewa suna daga cikin sojojin masu tsaron kasar Iran a wajen gwamnatin kasar.

Ma’aikatar harkokin wajen ta kara da cewa, ta dauki wannan matakin maida martani ne dai dai da dokar kasar ta shekara 2019 wacce ta sanya sojojin Amurka cikin sojojin yan ta’adda, kamar yanda tayi da IRGC.

Dakar wacce majalisar dokokin kasar Iran ta kafa ashekara 2019 ta bayyana cewa duk wata kasa wacce ta yi abinda Amurka ta yin a sanya IRGC cikin yanta’adda ita ma tana cikin wadannan kasashe.

Dai dai da wannan dokar JMI tana daukar Sojojin Ruwa na kasar Agentina da sojojinta na sama a matsayin kungiyoyin yanta’adda a wajenta.

Daga karshe bayanin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya kammala da cewa gwamnatin kasar Agentina ce da al-hakin duk abinda zai faru da sojojinta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted