Iran: Tataccen Uranium Ko Kadan Ba Zai Fita Daga Kasar Ba

Sakataren majalisar tsaron kasar Iran Mohsen Rizaei ya  ce Iran ba zata amince makamashin Uranium wanda aka tashe a cikin gida ya bar kasan ba,

Sakataren majalisar tsaron kasar Iran Mohsen Rizaei ya  ce Iran ba zata amince makamashin Uranium wanda aka tashe a cikin gida ya bar kasan ba, kuma ko menene karancinsa.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Rezaei yana fadar haka a lokacinda yake hira da tashar talabijan ta Almayadden ta kasar Lebanon a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa, Iran zata yi amfani da taceccen Uranium na kasar don amfanin kanta.

Ya ce, gwamnatin JMI ta Iran ta fadawa Rasha kan cewa, ba zata mika tataccen uranim da ke wajenta bay a fice daga kasar ba. Nata ne kuma ita zata yii amfani da shi. Ya kara da cewa Iran tana bukatar tataccen makamashin Uranium don gina jiragen ruwa na kasuwanci da kuma na yaki wanda ake kira submerin. Don haka ba zata mika shi ga wata kasa ba.

Daga karshe ya bayyana cewa, duk wani yakin da Amurka da kawanta zasu fara, zai game dukkan kasashen yankin daga ciki har da kasar Lebanon mai yuwa har wajensa.

Wannan yana zuwa ne a dai dai lokacinda JMI ta bayyana sharuddanta na kawo karshen yaki da AMurka. Daga ciki har da kawo karshen yaki da ita da kawaynta daga ciki har da kasar Lebanon.

Banda haka akwai dagewa kasar dukkan takunkuman da aka dora mata, da sakin kudadenta da aka sace, dauke hana zirga zirgan jiragenta ta ruwa da kuma lamuni kan baza’a sake kai mata wasu hare haren ba.

Ya yimaganar ci gaban da JMI ta samu a fagen kayakin yaki, wadanda suka hada da na kayakin lantarki, wanda ya kai ga tana kwace sarrafa jiragen yakin Amurka, ta sauke su kasa ba tare da sun lalace ko an kakkabosu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted