Wasu manya manyan jiragen dakon man fetur guda biyu sun sabawa dokokin wucewa a mashigar ruwa ta Hurmuz amma sun tsira daga haramtasu daga shigowa yankin kwata kwata.
Kamfanin dillancin labaran MehrNews na kasar Iran ya bada labarin cewa hukuma mai kula da zirga zirgan jiragen ruwa a mashigar ruwa ta Hurmuz ta bada sanarwan kama manya manyan jiragen ruwa masu dakon man fetur a mashigar ruwa ta Hurmuz, wadanda suke kokarin sace hanyar wucewa.
Labarin ya kara da cewa, kamfanonin jiragen guda biyu, kamar yanda dokokin hukumar suke, sun rubutawa hukumar wasika suna neman afwa, kan laifukan da suka aikata. Wanda hakan ya sa hukumar bata sanya su cikin wadanda zata haramta masu shiga yankin ba.
Amma zata hukuntasu kamar yanda dokokin suka tanadar.
Banda haka labarin ya bayyana cewa jiragen sun gabatar da takardun karya dangane da jiragen nasu da kuma wasu abubuwan da suka aikata.