Iran ta bukaci MDD da Hukumar kula da makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) da su yi Allah wadai da shirin Amurka na neman bayyanai kan shirin nukiliyar Tehran.
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi kira ga bangarorin biyu da su Yi Allah Wadai Da tayin da gwamnatin Amurka ta yi na dala miliyan 20, domin samun bayanai kan shirin nukiliyar Iran.
Ya yi gargadin cewa wannan kudirin zai iya karfafa leken asiri da kuma jefa masana kimiyya da cibiyoyin nukiliya cikin hadari.
A cikin wata wasika da aka aika wa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, da Shugaban Kwamitin Tsaro Sanita Pavļuta-Deslandes, da Darakta Janar na IAEA Rafael Grossi, Araghchi ya bayyana sanarwar Amurka a matsayin barazana ga tsaro da shirin nukiliyar farar hula na Iran.
A ranakun 6 da 7 ga Nuwamba Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da Rundunar Sojojin Amurka a yammacin Asiya, suka bada sanarwar ladan Dala Miliyan 20 ga wanda ya kwarmata musu wani abu game da shirin nukiliyar Iran.
Amurka na neman bayanai game da shirin da ma’aikata da ke da alaka da shi, da kimiyya, wurare, da kayan aiki.
A cikin wasikarsa, Mista Araghchi ya bayyana sanarwar a matsayin abin tsoro, yana mai jaddada cewa a bayyane take karfafa tattara bayanan sirri kan cibiyoyin nukiliya, kayan aiki, kayan fasaha, da ma’aikatan kimiyya. Mista Araghchi ya bayyana cewa wannan tayin ya kuma sanya shakku kan sahihanci, mutunci, da amincin tsarin kariya na hukumar IAEA, musamman lokac