Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Iran ta yi Allah Wadai da gwamnatin Faransa da ‘yan sanda kasar kan tsauraran Matakai na murkushe masu zanga-zangar da aka gudanar a fadin Faransa kan tsardar rayuwa da hauhawar farashin makamashi da tabarbarewar ayyukan gwamnati.
A wata sanarwa da ta fitar hukumar ta bayyana cewa gwamnatin Faransa da ‘yan sanda sun take hakkin masu zanga-zangar da suka fito kan tituna don yin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da tabarbarewar ayyukan gwamnati.
Amfani da karfi, kame masu zanga-zanga 448 da amfani da hayaki mai sa hawaye da sauran matakan danniya don tarwatsa tarurrukan lumana na cikin ababen da suka keta hakkin ‘yancin fadar albarkacin baki.
Saboda haka, gwamnatin Faransa, na da alhakin girmama, karewa, da kuma tabbatar da wadannan hakkokin yadda ya kamata, inji sanarwar hukumar kare hakkin bil adama ta Iran.
Wadannan kalamai suna nuni ne ga sukar da jami’an Faransa suka yi wa matakan da gwamnatin Iran ta dauka a lokacin rikicin da ya barke a farkon watan Janairun 2026. A lokacin, Faransa tana cikin kasashen farko