Iran ta yi watsi da zarge-zargen da ta danganta da “marasa tushe da nuna mugunta” da gwamnatin Faransa ta yi game da hare-haren intanet da aka kai wa manyan kantunan Turai.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da wannan da wannan zargin da aka yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Paris na kokarin nuna gazawarta a harkokin mulkin cikin gida ga Tehran.
Sanarwar ta yi nuni da yunkurin gwamnatin Faransa na dora alhakin abubuwan da suka faru a kan intanet wanda ya haifar da dumamar akwatinan sanyaya abinci wato firiji da asarar abinci da aka kiyasta ya kai na miliyoyin Yuro.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa irin wadannan zarge-zargen kawai hasashe ne na gazawar Faransa na biyan bukatun ‘yan kasarta.
A ranakun 11 da 12 ga Oktoba, an kai hari kan daruruwan manyan kantuna a fadin Faransa ta hanyar hare-haren yanar gizo.
An kara yawan zafin firiji da injinan daskararda kayan abinci daga nesa.
An kuma bayar da rahoton fuskantar irin hakan a akalla wasu kasashen Turai 11.
A martanin da ya mayar, Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya kira jakadan Iran, inda ya yi gargadin cewa Paris “ba ta kawar da yiwuwar daukar matakan ramuwar gayya.