Ma’aikatar leken asiri na kasar Iran ta bada sanarwan wargaza wasu tawagogin yan ta’adda dauke da makamai guda biyar da kuma wasu guda uku masu fasa korin makamai zuwa cikin kasar a lardunan Albus da Tehran da kuma Kermanshah.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar tana fadar haka a yau Laraba, ta kuma kara da cewa, ta sami nasarar kama wadan nan yan ta’adda ne tare da taimakon Jama’a na wadannan yankunan wadanda suka tseguntawa ma’aikatar dangane da shirin yan ta’addan na kai hare hare a cikin wadannan yankuna.
Labarin ya kara da cewa, Amurka da HKI sune suke tallafawa wadannan kungiyon don kai hare hare da kuma rikita kasar Iran ta yanda zasu sami damar kifar da gwamnatin kasar.
Banda haka bayanin ya kara da cewa, jami’an tsaro na ma’aikatar sun sami nasarar kama tawagogi guda uku wadanda suka yi kokarin shigo da makamai kasar daga kan iyakar kasar da Lardin Kurdistan wanda bai sami nasar ba. Bayanin ya kara da cewa, an kwace bindigogi gud 50 da kuma magazin magazin na albarusai har guda 100 daga hannun masu fasakorin.