Kakakin Majalisar Dokokin Iran ya bayyana cewa: Sabon birnin makamai masu linzami sako ne bayyananne daga Iran ga makiyanta
Kakakin Majalisar Dokokin Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya tabbatar da cewa: Sabon birnin makamai masu linzami da Iran ta gina sako ne bayyananne daga Iran ga maƙiyanta.
A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Qalibaf ya bayyana a cikin wani sako bayan bayyana sabon birnin makamai masu linzami na Iran cewa: “Bayyana sabon birnin makamai masu linzami mallakar rundunar sojin sama ta kare juyin juya halin Musulunci ta nuna jajircewar al’ummar Iran na kare ‘yancin kai, tsaro, da kuma cikakken yankin ƙasarta.
Abin da aka bayyana a yau shi ne ƙarshen shekaru na ƙoƙari na masana kimiyya da injiniyoyi, ƙwarewar kwamandoji, da kuma sadaukarwar mayaƙa waɗanda suka dage dare da rana a ƙarƙashin mawuyacin hali, wanda ya kawo wannan muhimmin aiki ga nasara.”
Ya ƙara da cewa, “Yana miƙa godiya da jinjinawa ga duk waɗannan abokan aikina, musamman matasa waɗanda suka ba da gudummawa wajen ci gaba da wannan nasara ta hanyar dogaro da ƙwarewar cikin gida da karfafa ruhin jihadi”.