Ministan Harkokin Wajen Iran ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta yi Allah wadai da tayin Amurka na bayar da lada ga duk wanda ya bayar da bayanai kan shirin Makamashin nukiliya na Iran
A cikin wata wasika da ya aike wa Antonia Guterres, Kwamitin Tsaro da Grossi, Araqchi ya yi kira da a yi Allah wadai da “sanarwar da Amurka ta yi” wadda ta bayar da lada har zuwa dala miliyan 20 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan shirin makamashin nukiliyar Iran.
Kamfanin dillancin labaran Mehr ya ruwaito cewa: Ministan Harkokin Wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya rubuta a cikin wata wasika zuwa ga Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, Shugaban Kwamitin Tsaro Sanita Paulota-Dislandes da Darakta Janar na Hukumar IAEA Rafael Grossi, game da “sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayar na bada lada har zuwa dala miliyan 20 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya”: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nemi Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kwamitin Tsaro da Darakta Janar na Hukumar IAEA su yi Allah wadai da wannan sanarwar da Amurka ta yi ba tare da wata shakka ba.”