Iran Ta Yi Gargadi Kan Duk Wani Gigi Na Sake Kai Mata Hari

Ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da wani sabon sashe na makamai masu linzami mallakar Rundunar Sojojin Sama ta Iran.

Babban Hafsan Sojojin Iran, Manjo Janar Ali Abdullahi, ya yi gargadi ga makiya na sake kai hari, wanda ya ce abubuwan mamaki za su biyo baya daya bayan daya idan har makiyan sukayi wnanan kuskuren.

Ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da wani sabon sashe na makamai masu linzami mallakar Rundunar Sojojin Sama ta Iran.

Janar Abdullahi ya yaba da rawar da sojojin suka taka a tsaron kasar, yana mai kiran membobin Rundunar Sojojin Sama ta Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), da kuma dukkan ma’aikatan sojojin Iran, a matsayin jarumtattu.

A cewarsa, Iran ta cimma wata gagarumar nasara a kan makiyanta, duk da cewa Amurka ta tura manyan makamai, wadanda da kayan aikin soja, da ba a taba gani ba a cikin rikicin da ya dauki lokaci mai kama da haka.

Ya ce, “A cikin rikici na gaba, abubuwan mamaki za su zo daya bayan daya.”

Wannan sabon wurin da aka bude wani bangare ne na kayayyakin aikin makamai masulinzami na Rundunar Sojojin Sama ta IRGC, zai tallafawa da kuma taimakawa wajen ci gaba da shirye-shiryensu na yaki da barazanar da ka iya tasowa.

Da yake mayar da martani ga kalaman da FiraMinistan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi kwanan nan—cewa ko dai Isra’ila ta lalata Iran, ko kuma Iran ta lalata Isra’ila—Janar Abdollahi ya jaddada cewa wannan ba sabon abu ba ne, ya ce makiya sun nemi lalata Jamhuriyar Musulunci ta Iran, amma sun gaza, yana mai bayyana Amurka da gwamnatin Isra’ila a matsayin manyan masu asara a fagen daga.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted