Ƙwararru A Bangaren Yancin Addini Na MDD  Suna Ziyarar Aiki A Tarayyar Najeriya

Manyan jami’an Majalisar Dinkin Duniya kan ‘yancin addini sun fara  wata ziyarar makwanni biyu a Najeriya a ranar Litinin, bayan zargin kasar da muzgunawa mabiya

Manyan jami’an Majalisar Dinkin Duniya kan ‘yancin addini sun fara  wata ziyarar makwanni biyu a Najeriya a ranar Litinin, bayan zargin kasar da muzgunawa mabiya addinin kirista a shekarar da ta gabata.

A yayin da Amurka ta zafafa lamarin, wanda take ganin an tauyewa mautane damarmaki na gudanar da hakkokin dake kansu na addini da na siyasa, lamarin da ya sanya gwamnatin kasar daukar tsauraran matakai na kai hare-hare ba kakkautawa a kan wadanda ke ikrarin jihadi.

Tuni dai Amurka ta tura dakarun ta zuwa kasar tare da mika bukatar sake mayar da hankali kan fatattakar mayakan da ke da alaka da kungiyar IS a yankin.

Masu bincike sun ce abin da ke faruwa a kasar mai mafi yawan al’umma a Afirka, hankali ya fi karkata ne akan masu ikrarin jihadi dake da matukar karfi a arewacin kasar da ke da mafi rinjayen musulmi, kuma hakan ke nuni da cewa galibin wadanda abin yafi shafa musulmi ne.

A yayin wannan ziyarar, mai ba da rahoto na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan ‘yancin yin addini Nazila Ghanea, za ta ziyarci Abuja fadar gwamnatin Najeriya, da Kano cibiyar kasuwancin arewacin ƙasar da kuma birnin Jos dake jihar Filato mai ɗauke da mabiya addinai mabambanta.

A wadannan ziyarce-ziyarcen ne Ghanea tace za a iya fahimtar musabbabi faruwar rudanin da ya dabaibaye wannan kasa mai tarin al’umma dake kawo cikas musamman akan abin da ya shafi ‘yancin tafiyar da lamuran addini.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted