Zimbabwe: Majalisa ta amince da tsawaita wa’adin shugabancin kasa

Majalisar dokokin Zimbabwe ta amince da kudirin tsawaita wa’adin shugabancin kasa. Hakan ya share fagen tsawaita wa’adin shugaban kasa da na majalisar dokoki daga shekaru

Majalisar dokokin Zimbabwe ta amince da kudirin tsawaita wa’adin shugabancin kasa.

Hakan ya share fagen tsawaita wa’adin shugaban kasa da na majalisar dokoki daga shekaru biyar zuwa bakwai.

Gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin Zimbabwe, wanda zai tsawaita wa’adin shugabancin kasa da shekaru biyu, yanzu yana bukatar sa hannun Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ne kawai don fara aiki.

Saidai matakin ya fuskanci suka mai zafi daga ‘yan adawa a kasar inda jam’iyyar Zanu-PF mai shekaru 83 ke da rinjaye a majalisar dokoki.

Majalisar dokokin ta amince da gyare-gyaren da Majalisar Dattawa ta gabatar lokacin da ta amince da sabuwar dokar a ranar 24 ga Yuni, in ji Kakakin majalisar.

Masu adawa sun bayyana matakin a matsayin “juyin mulki wa kundin tsarin mulkin kasar”.

Wannan yana nufin cewa wa’adin Mnangagwa na karshe a cikin wa’adi biyu da kundin tsarin mulki ya tanada za a tsawaita shi har zuwa 2030.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted