Ministan Harkokin Wajen Iran ya gana da takwaransa na Pakistan a kasar Kyargyzistan
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da takwaransa na Pakistan Mohammad Ishaq Dar, a gefen taron ministocin harkokin waje na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a Kyargyzistan, inda suka yi tattaunawa ta bangarorin biyu.
Kamfanin dillancin labaran “IRNA” ya ruwaito cewa: Ministan Harkokin Wajen Iran ya isa Cholpon-Ata, Kyargyzistan, a ranar Alhamis da yamma don halartar taron ministocin harkokin waje na SCO.
A jawabinsa ga ministocin harkokin wajen kasashe, Araqchi ya jaddada bukatar da ke akwai ta wuce hadin gwiwa ta siyasa da tsaro zuwa ga hadin gwiwa mai cikakken tsari wanda ya kunshi fannoni na tattalin arziki, fasaha, da ci gaba. Ya lura cewa shiru da kuma nuna fuska biyu game da hare-haren da ake kai wa Iran na kara wa masu kai hare-haren kwarin gwiwa su maimaita laifukansu.
A gefen taron, Araqchi ya kuma gana da takwarorinsa na wasu kasashe mambobin kungiyar, ciki har da ministocin harkokin waje na Belarus da Rasha, kuma ya yi tattaunawa da su.