Baqa’i: Dole A Hukunta Kasashen Makwabtan Iran Da Suka Taimakawa Amurka A Yaki

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Dole ne a hukunta kasashen da suke makwabtaka da Iran da suka yi tarayya da Amurka a

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Dole ne a hukunta kasashen da suke makwabtaka da Iran da suka yi tarayya da Amurka a kaddamar da hari kan Iran

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada bukatar a dora alhakin ikirarin Amurka na hannun kasashen da suke makwabtaka da Iran a hare-haren sojin da aka kai wa Iran, yana mai cewa kare kai da Iran ke yi na nufin dawo da tsaro da kwanciyar hankali ga yankin baki daya.

Kakakin ya wallafa wani bidiyo dauke da kalamai daga kwamandan rundunar sojin Amurka ta tsakiya (CENTCOM), wanda ya ambaci hadin gwiwa da kuma shigar kasashen yankin biyar da Jordan a hare-haren soja da aka kai wa Iran. Baghaei ya rubuta cewa: “Kwamandan rundunar sojin Amurka ta tsakiya ya bayyana sunayen kasashe biyar na yankin Tekun Pasha da Jordan a fili, yana mai cewa sun shiga cikin hare-haren soja da Amurka ta kai wa Iran.”

Baqa’i ya kara da cewa: “Idan wannan ikirarin Amurka karya ne, ya kamata gwamnatocin da aka ambata su fito su musanta hakan a hukumance kuma a bayyane.”

Baqa’i ya ƙara da cewa: “Bai kamata a manta cewa: Babban tushen rashin tsaro da rikici a yankin, ba wani abu bane illa farmakin sojojin Amurka da na Sahayoniyya kan Iran. Duk wani shiga cikin wannan farmakin, gami da samar da dandamali don ayyukan soji, ya zama aikin ta’addanci, bisa ga kuduri mai lamba 3314, wanda ya bayyana farmakin, da kuma keta ƙa’idar kyakkyawar maƙwabtaka da kuma Mataki na 2, Sashe na 4, na Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted