Mataimakin ministar harkokin wajen kasar cuba Carlos De Cosio ya ce; duk wani hari na soja da Amurka za ta kai wa kasarsa, zai zama bude yaki ne mai hatsari, sannan ya kara da cewa zai yi sanadiyyar kashe rayuwa da barna.
Bugu da kari, ministan harkokin wajen na Cuba ya ce, hari irin wannan zai jaza wa Amurka asara masi yawa.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta cuba ya kuma ce, tunshen sabanin shi ne yadda Amurka ta ki amincewa da kasar cuba ta zama kasa mai cin gashin kanta.
Wannan gargadin na mataimakin ministan harkokin wajen Cuba, yana zuwa ne adaiddai lokacin da kasar take fuskantar matsalar makamashi da yankewar wutar lantarki, haka nan kuma tsayawar hanyoyin sadarwa da ya hada da Internet.
Kasar ta Cuba dai tana fuskantar takunkumin makamashi da Amurka ta kakaba ma ta, tare da hana a kai ma ta man fetur daga kasar Venezuela. Bugu da kari Amurkan tana barazanar kai wa kasar ta Cuba hari.