Iran: Mutane  4 Sun Yi Shahada Sanadiyyar Harin Ta’addancin Amurka A Ahwaz

Mutane 4 sun yi shahada yayin da wasu 5 su ka jikkata sanadiyyar harin ta’addanci da wuce gona da iri da Amurka ka kai da

Mutane 4 sun yi shahada yayin da wasu 5 su ka jikkata sanadiyyar harin ta’addanci da wuce gona da iri da Amurka ka kai da makamai masu linzami a gefen garin Ahwaz dake kudu maso yammacin Iran.

Mataimakin gwamnan gundumar Khuzistan akan harkokin tsaro Waliyullahi Hayati ne ya bayar da labarin abinda ya faru sanadiyyar harin na Amurka.

Har ila ya Waliyullah ya ce a halin yanzu ana gudanar da bincike akan hakikanin abinda ya faru, kuma masu ayyuka ceto da agaji suna gudanar da ayyukansu a wurin.

Haka nan kuma ya ce a nan gaba za fitar da bayani akan wasu Karin bayanai da kuma yanayin da wadanda su ka jikkata suke ciki.

A cikin sa’oi 24 da  su ka gabata Amurka ta kai hare-hare har sau 12 a cikin sassa mabananta na gundumar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted