Luguden wuta kan yankunan Falasdinawa da tashin gobara a yankunan daban-daban na Gaza
Rahotonni sun ruwaito cewa: Jiragen saman yakin sojin mamayar Isra’ila sun kai hare-hare a yammacin Alhamis, inda suka lalata gidaje a sansanin ‘yan gudun hijira na Bureij da ke tsakiyar yankin Gaza, sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliya a arewa, da unguwannin Zeitoun da Jalaa na birnin Gaza, da kuma sansanin ‘yan gudun hijira na Maghazi, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane da dama.
Hotunan kai tsaye sun nuna gine-gine da suka lalace, gobara tana tashi da ramuka a ƙasa a wuraren da aka kai hare-haren. Rahotonnin sun bayyana wadannan a matsayin hare-haren sama mafi girma da aka kai a yankin Gaza tun bayan tsagaita wuta.
Wani mai magana da yawun rundunar tsaron farar hula a Gaza ya shaida cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun bayar da umarnin barin gidaje a yankuna shida na yankin Gaza a cikin ‘yan awanni kadan.
Wata majiya a Asibitin Baptist ta ruwaito cewa: Falasdinawa da dama sun ji rauni a wani harin sama da sojojin Isra’ila suka kai kan wani gini a unguwar Zeitoun, kudu maso gabashin birnin Gaza.
Majiyoyin yankin sun bayyana cewa: An samu raunuka sakamakon harin sojojin Isra’ila da suka kai kan hedikwatar kungiyar Musulunci a sansanin ‘yan gudun hijira na Maghazi da ke tsakiyar yankin Gaza.