Kakakin rundunar sojan jamhuriyar Musulunci ta Iran Birgediya Janar Akrami Niyah ya ce:Iran za ta yi amfani da sabbin dabaru da salon a yaki idan har aka kawo wa muhimman cibiyoyinta hari a kudancin kasar.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto kakakin rundunar sojan na Iran yana cewa; Bayan da Amurka ta keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta, yanzu an shiga wani sabon shafi na yaki, haka nan kuma rundunar sojan Iran tana mayar da martani akan abokan gaba, kuma za ta ci gaba da hakan matukar Amurkawa suna kai wa cibiyoyin Iran hare-hare a gabar ruwan tekun pasha.
Haka nan kuma ya ce, ya kamata Amurkawa su kwana da sanin cewa ba za su ci gaba da abinda suke yi ba na lokaci mai tsawo,idan kuwa su ka ci gaba da kaiwa kudancin kasarmu hare-hare, to kuwa za mu dauki sabbin matakai.
Har ila yau ya ce, tuni an tsara matakan da za a dauka akan haka wanda zai tilastawa abokan gaba dakatar da yakin.
Kakakin rundunar sojojin na Iran ya kuma ce; A lokacin da ya dace za a ga sabbin matakan da aka tsara.
Dangane da batun daukar fansa akan jinin shahidai, kakakin rundunar sojan na Iran ya ce; Batun daukar fansa ya zama wata bukata ce ta al’ummar kasar Iran.