Kakakin Majalisar Dokokin Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin Yahudawan Sahayoniyya ita ce babbar maƙiya ga dukkan ƙasashen Musulunci
A lokacin ganawarsa da Fira Ministan Iraki a Tehran, Kakakin Majalisar Dokokin Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Babu shakka Yahudawan Sahayoniyya sune manyan makiya ga dukkan kasashen Musulunci. Ya jaddada cewa, hadin gwiwa tsakanin Iran da Iraki wajen kiyaye hadin kan kasashen Musulunci a kan wadannan maggan halittu, wadanda suka fito fili suna bayyana matsayinsu na kasancewa manyan makiya Musulunci da Musulmai a duniya, yana da matukar muhimmanci kuma yana da tasiri.
A cewar kamfanin dillanci na “IRNA”, bangarorin biyu sun yi nazari kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a lokacin taron. Qalibaf ya bayyana godiyarsa ga al’ummar Iraki da gwamnatin kasar bisa gudanar da jana’izar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, a biranen Iraki. Ya kuma yaba da karamcin da suka nuna wa masu ziyarar taron ranar Arba’een na Imam Husain {a.s}.
Qalibaf ya jaddada alaka mai zurfi tsakanin Iran da Iraki, yana mai cewa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu yana da matukar tasiri wajen inganta zaman lafiya a yankin da kuma duniyar Musulunci. Ya kara da cewa tare za su iya magance matsalolin yankin da dama.
A nasa bangaren, Fira Ministan Iraki ya isar da gaisuwar al’ummar Iraki da gwamnatin kasar ga kakakin Majalisar Dokokin Iran da kuma al’ummar Iran, yana mai tabbatar da cewa kasashen biyu ba wai kawai suna da kusancin yanki ba, har ma da kawance da makoma iri daya.