Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Babu wani aikin neman kera makamin nukiliya a Dutsen Kaleng, don haka Iran za ta kalubalanci duk wani hari kan yankin
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Hare-hare da barazanar da Amurka ke yi wa cibiyoyin makamashin nukiliya na Iran na zaman lafiya ba wai kawai sun karya dukkan ka’idoji da tushe na Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa ba ne, da kuma kudurorin Kwamitin Gwamnonin hukumar cibiyar kula da makamashin nukiliya ta IAEA kawai, Manyan Tarurruka, da kudurorin Kwamitin Tsaro Majalisar Dinkin Duniya dadaddu sun zama hujja mai karfi ta nuna kiyayyar Amurka ga Shirin kimiyya da ci gaban Iran.
Dangane da hare-haren da Amurka ke kai wa cibiyoyin makamashin nukiliya na Iran, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya rubuta a dandalin X cewa: “An bayyana ayyukan makamashin nukiliya na Iran ga Hukumar IAEA bisa ga wajibai na kariya. Mayar da hankali kan Dutsen Kalang, inda babu wani aikin kera makaman nukiliya da ake yi, ba komai ba ne illa neman hanyar lalata ci gaban Iran da rusa harkokin fasaharta.”
Baqa’i ya jaddada cewa: Iraniyawa za su tsaya tsayin daka kan duk wani hari da Amurka ke kaiwa kan ‘yancin kasarsu da tsaron kasa.