Zanga zanga Tsadar Rayuwa Na Yaduwa A Turai

A Portugal, dubban ma'aikata sun yi zanga-zanga a Lisbon don neman karin albashi da fansho.

Dubban mutane sun yi zanga-zanga a wannan Lahadi, a Portugal da Faransa don neman karin albashi, samar da gidaje masu sauki, da kuma tsadar rayuwa.

Rahotanni sun ce an ci gaba da zanga-zangar tsadar rayuwa da rashin daidaiton zamantakewa a fadin Turai a ranar Asabar, tare da zanga-zangar a Portugal, Spain, da Faransa.

A Faransa, an gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa, don neman inganta harkar ilimi ga dalibai a ranar Asabar ta shida a jere, duk cewa, halartar jama’a a zanga zangar ya ragu idon aka kwatanta da makonnin baya.

A Portugal, dubban ma’aikata sun yi zanga-zanga a titunan Lisbon don neman karin albashi da fansho, gidaje masu araha, da kuma inganta ayyukan gwamnati.

An gudanar da zanga-zangar ce, bisa kiran babbar kungiyar kwadago ta kasar, CGTP-IN.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted