Kasashen Masar, Sudan da Eritrea, sun cimma matsaya ta tabbatar da tsaro a yankunansu.
Bangarorin sun bayyana hakan ne bayan taron da ministocin harkokin wajensu suka gudanar a gefen taron Aswan na shida don Zaman Lafiya da Ci Gaba Mai Dorewa.
An gudanar da taron bangarori uku tsakanin Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty da takwaransa na Sudan, Mohi El-Din Salem, da takwarorinsu na Eritrea, Osman Saleh.
Tsaro a Tekun Maliya, da kuma kin amincewa da tallafawa kungiyoyi masu dauke da makamai daga kasashen waje a Sudan su ne ginshikin taron bangarori uku.
Da suke sake tabbatar da alakar tarihi tsakanin kasashensu, ministocin sun yi alkawarin karfafa shawarwari da hadin kai kan batutuwan da suka shafi kowa, da nufin tallafawa tsaron yanki da kwanciyar hankali da kuma biyan bukatun jama’arsu, a cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta fitar.