Isra’ila Ta Hana Dubban kwantenonin Kayan Agaji Shiga Gaza

gwamnatin isra'ila tana kwantenoni dubbai shiga yankin gaza da kayayyakin agaji da tantuna

Ministan harkokin wajen kasar Turkiya Hakan Fidan ya bayyana cewa gwamnatin yahudawan sahyuniya ta hana shigar da dubban tanti –tanti na wucin gadi a yankin Gaza da haka ya sa falasdinawa suke zama cikin hadarin ambaliyar ruwa, guguwa da kuma yanayin mai tsananin sanyi

A wata hira da yayi da TGRT fidan ya bayyana cewa isra’ila tana toshe dubban kwantenoni dake dauke da tanti-tanti na wucin gadi a yankin Gaza a daidai lokacin da amabliyar ruwa ta kara jefa falasdinawa cikin mawuyacin hali , kuma ya kara ta’azzar matsalolin rayuwa a yankin

Haka zalika fidan yayi bayani cewa shugaban kasar Turkiya Rajjab tayyib Ardigan ya bada umarni a aike da tant-tanti na wucin gadi zuwa ga alummar falasdinu dake Gaza, turkiya tana da dubban kwantenoni da aka yi amfani da su bayan girgizar kasa da aka yi da ardigon ya bada umarni a aika da su zuwa gaza a rana ta farko.

Daga karshe ministan harkokin wajen ya kara da cewa al’ummar falasdinu suna bukatar kwantenonin din cikin gaggawa yace an tilasta musu rayuwa cikin mawuyacin yanayi da suke fuskantar ambaliyar ruwa da kuma tsananin sanyi

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted