Yan majalisar Faransa Sun Bukaci A Haramta Amfani Da Tiyagas

yan majalisa a kasar faransa sun bukaci a haramta amfani da tiyagas kan masu zanga zanga saboda illarsa

Rahotanni sun bayyana cewa yan majalisa a kasar Faransa da masu rajin kare hakkin bil adama sun bukaci a harmata amfani da hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zangar saboda matsalar dake jawowa ga lafiya.

Rahotanni sun bayyana cewa yan majalisar da masu rajin kare hakkin bil adama sun gabatar da wannan bukatar ne bayan zanga-zangar da aka yi a baya bayan nan, inda suka bukaci jami’an yan sanda su dakatar da amafani da tiyagas saboda matsalar da yake  haifarwa musamman ma ga lafiya

kungiyoyin sun ce sun samu korafe –korafe fiye da 10,000 game da wannan batun, wannan yasa yan majalisa daga jam’iyar bangaren hagu ta jean luc wanda ke neman takarar shaugbancin kasa suka yi kira da a haramta amfani da hayaki mai sa hawaye, tare da gudanar da bincike mai zaman kansa kan illolin da zai iya haifarwa ga lafiyar mata

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted