Majiyoyin lafiya a Gaza sun ce Falasdinawa uku sun rasa rayukansu, kana wasu hudu kuma, ciki har da yaro daya, sun jikkata a hare-haren Isra’ila a fadin Zirin.
An kashe wani mutum mai shekaru 50 lokacin da wani jirgin saman Isra’ila mara matuki ya jefa bam kusa da mahadar Al-Matahin, gabashin Deir al-Balah a tsakiyar Gaza.
Wani Bafalasdine ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a harin da Isra’ila ta kai kan sansanin ‘yan gudun hijira a Al-Mawasi, a yammacin Khan Younis, yayin da na uku ya mutu sakamakon raunukan da ya samu sakamakon harin jiragen sama mara matuki a kudu maso yammacin birnin.
An harbi wani yaro mai shekaru 12 a baya lokacin da sojojin Isra’ila suka bude wuta a tsakiyar Khan Younis, yayin da Falasdinawa uku suka jikkata a wani harin jiragen sama mara matuki daban a Bir al-Naaja, yammacin Jabalia, a arewacin Gaza.
Hare-haren sun nuna yadda Isra’ila ke ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da ka cimma a baya.
A wani labarin kuma Falasdinu ta yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen goyon bayan gwamnatin Isra’ila ga ‘ta’addanci’ kan ‘yan gudun hijira a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.