Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Manjo Janar Mohsen Rezaei, ya tabbatar da cewa tsarin duniya ya canza sosai, yana mai jayayya cewa ba za a iya kwatanta Iran ta yau da ta shekaun baya ba.
A cikin wani rubutu da ya yi a shafin X, Janar Rezaei ya bayyana cewa Iran ta 2026 ba Iran ce ba ta 1943 ko 1945.
Ya bayyana Amurka a matsayin kasa “da ta sha kaye” maimakon wata kasa mai nasara, ya kara da cewa duniya ta canza kuma “ba za a iya rage tsarin da ake da shi a yanzu da tsoffin hotuna ba.”
Taron Tehran a shekarar 1943 ya hada shugabannin Amurka, Burtaniya, da tsohuwar Tarayyar Soviet don daidaita dabarun yakinsu, yayin da Taron Yalta a shekarar 1945 ya taimaka wajen tsara tsarin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu. Janar Rezaei ya yi wadanan kalamman ne bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya yada wani hoto a shafinsa na Truth Social a ranar Asabar yana kwatanta taron Yalta na 1945 da taron da ya yi kwanan nan da shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.