An Watse A Taron COP31 Ba Tare Da Cimma Matsaya Ba

Kasashen Rasha da Saudiyya na cikin kasashen da ke adawa da duk wani ambaton man fetur a cikin takardar karshe.

A Turkiyya an waste a tattaunawar MDD kan sauyin yanayi na COP31 ba tare da cimma wata matsaya ta azo a gani ba kan matsalolin dake haifar da dumamar yanayi.

Ainihin sabanin da ke tsakanin bangarorin biyu shi ne batun babban abin da ke haifar da dumamar yanayi, wanda kasashe da dama ke son a ambata a daftarin karshe.

Tsawon makonni biyu, wakilai sun yi kokarin daidaita matsayinsu kan alkawarin magance dumamar yanayi da kuma kudaden da ake bukata don yaki da sauyin yanayi, saidai bambance-bambancen sun yi matukar tasiri wanda ya sanya ba’a cimma matsaya a zahiri ba.

Kasashe da dama, da kuma Tarayyar Turai da kasashe 27 mambobi, sun yi watsi da daftarin da shugaban kasar Turkiyya da Ostiraliya suka gabatar, musamman saboda rashin ambaton man fetur a fili.

Duk da haka, wasu wakilai sun fi bukaci samun sulhu, suna ganin ya fi kyau a cimma matsaya, ko da kuwa ta wucin gadi ce, fiye da a watse ba tare da wata yarjejeniya ba.

Kasashen Rasha da Saudiyya suna cikin kasashen da ke adawa da duk wani ambaton man fetur a cikin takardar karshe.

Wannan rashin cimma matsaya ya zo ne a lokacin da batun man fetur ke taka muhimmiyar rawa a tattaunawar yanayi ta duniya.

Tsawon shekaru sama da 25, batutuwan da aka gabatar daga taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya ba su taba yin magana a kan wadannan hanyoyin samar da makamashi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted