Dakarun kare juyin musulunci na iran IRGC sun sanar cewa dakarunsu sun yi nasarar kakkabo jirgin sama mara matuki na kasar Amurka wanda ake amfani da shi wajen leken asiri samfurin MQ-1 kuma karo na 20 da aka kakkabo tun bayan fara haramataccen yakin da Amurka da isra’ila suka kaddamar kan kasar iran
Ofishin hulda da jama’a na dakarun kare juyin musulunci ya fitar da wannan sanarwar ne a yau lahadi cewa jiragen yaki na tsaron sararin samaniya wanda ke amfani da sabon tsarin tsaron sararin samaniya na zamani sun harbor wani jirgin sama mara matuki na amurka kirar MQ1 wanda ke da karfin tashi mai dogon zango a gabashin mashigar ruwan Hormuz
Haka zalika ya kara da cewa wannan shi ne jirgi mara matuki na 4 wanda ake amfani da shi wajen leken asiri da kuma yakin soji na amurka wanda tsarin kare sararin samaniya na rundunar IRGC ya harbo a cikin saoi 24 da suka gabata
Daga karshe sun ce sararin samaniyar kasar iran jan layi ne ga dakarun sojin kasar , don haka duk wani wuce gona da iri ko keta sararin samaniya zai fuskanci mayar da martani mai tsanani kuma mai karfi