Rahotanni sun bayyana cewa kasar Iran ta shigar da kara kan amurka da wasu kasashen turai guda 4 sakamakon hari da Amurka ta kaddamar kan makarantar firamary a garin minab a kudancin kasar inda yayi sanadiyar mutuwar mutane 168 da suka hada da yara 123 dake da shekaru tsakanin 7 zuwa 12
Mataimakin shugaban kasar iran kan abubuwa da suka shafi dokoki Majid Ansari ya bayyana a yau lahadi cewa gwamnatin iran ta gabatar da hujjoji ga kotu a kasahen biyar da wasu shari’oi da tuni aka shigar da su da kuma wasu dake ci gaba da rijistarsu
Ansari ya kara da cewa ofishin kula da shari’a na gwamnati yana aiki da ministan shari’a da ministan harkokin waje da sauran bangarorin da suke sa ido kan harin da aka kai,
Daga karshe ya bayyana cewa game da batun matakin shari’a da za’a dauka kan kisan jagoran juyin musulunci na iran Ayatullah sayyid Ali Khamenai da sauran masana ilimin fasaha da kwamandojin soja da sauran fararen hula , da ma’aikatan jinya da yara kanana da kasar amurka da isra’ila suka yi, za su dauki matakin da ya dace ta hanyoyi daban-daban